Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Jami'an Jinya Sun Gudanar Da Zanga-zanga A Mexico


A kasar Mexico ma'aikatan jinya da dama sun yi zanga-zanga, su na bukatar hukumomin kasar su samar musu da kayan kare kan su daga kamuwa da cutar coronavirus, yayin da suke kula da masu cutar.

Jami’an sun tattare tituna a babban birnin kasar, su na zargin hukumomi da yin watsi da kare lafiyar su, inda aka ba su kayayyakin kare kai mararsa inganci.

Wata jami’ar jinya, Susan Ballesteros ta ce, ana umartar su da su sake amfani da uniform da takunkumin rufe fuska da ake amfani dashi fiye da sau daya, alhali 'yan uwansu da yawa sun kamu da cutar, wasu kuma sun mutu. Ta ce suna bukatar kayayyakin don su gudanar da aikin su kuma Jami’an jinya na bukatar hukumomi su saurare su.

Jami’an jinya sun dada kokawa da cewa duk da yawan aikin da ke kan su na kulawa da masu cutar coronavirus, ana kuma bukatar su ci gaba da koyar da daliban jami’a.

Kasar Mexico na da masu cutar COVID-19 sama da 70,000 kuma mutum 7,300 suka mutu a sanadiyyar cutar. Akasarin masu dauke da cutar sun fi yawa a bangaren birnin kasar da ke da cunkoson jama’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG