Kungiyar Taliban ta ayyana tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku albarkacin karamar Sallah wanda zai fara aiki daga yau Lahadi. Ta yi hakan ne ta wani sakon twitter wanda ta tura jiya Asabar, kuma Shugaban kasar ya ce ita ma gwamnatin kasar za ta mutunta tsagaita wutar.
Wwannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da yaki tsakanin bangaroron biyu ya kazance duk kuwa da annobar cutar corona
(Wasu mayakan Taliban tare da farar hula)
“Kar ku kai duk wani farmaki na soja kan abokan gaba a ko ina suke kuwa, idan abokan gaba su ka kai ma ku wani farmaki, ku kare kanku,” abin da mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid ya rubuta kenan ta kafar twitter. Ya kara da cewa saboda bukukuwan Sallar Idi kawai aka ayyana wannan tsagaita wutar wanda ke zuwa bayan karshen wata mai tsarki na Ramadan.
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya yi maraba lale da wannan kwance damara da Taliban ta yi sannan shi ma ya tabbatar masu da salama. “A matsayina na babban kwamandan askarawan kas ana umurci jami’an tsaron kasar Afghnistan da su mutunta tsagaita wutar na tsawon kwanaki uku, su kare kansu kawai idan an kai masu hari,” abin da Shugaban ya rubuta kenan ta kafar twitter.
Facebook Forum