Firaministan Burtaniya Boris Johnson na shirin rage rawar da kamfanin kera na’urorin sadarwar nan na kasar China mai suna Huawei a ayyukan kafa bangaren sadarwar Burtaniya na ingantaccen matakin nan na 5G saboda rikicin da ake tabkawa kan cutar coronavirus, a cewar jaridar Daily Telegraph.
Hasali ma, Johnson ya umurci jami’an da abin ya shafa a kasar da su bullo da wani shiri na rage rawar da kasarn China ke takawa a harkokin gina Burtaniya ta yadda zuwa shekara ta 2023 kasar China ba za ta taka wata rawa ba sam a harkokin gina madafun cigaba na Burtaniya, a cewar jaridar da daren ranar Jumma’a.
(Ginin kamfanin Huawei a Burtaniya)
Ana ganin Johnson zai so yin amfani da wannan mataki na rage tasirin China a Burtaniya wajen gamsar da Shugaban Amurka Donald Trump wajen tattauwar batutuwan cinakayya ganin cewa Burtaniya ta fice daga Tarayyar Turai, bisa ga bayanin jaridar.
Ofishin Firaministan na Burtaniya da ke Downing Street ya ki cewa komai bayan da aka tuntube shi. Haka shi ma kamfanin na Huawei ya ki cewa komai da aka nemi jin ta bakinsa.
Facebook Forum