Kasashe biyar, wadanda wasunsu sun taka rawa a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya a Afghanistan, sun gabatar da wata rubutacciyar takardar hadin gwiwa, mai yin maraba lale da tsagaita wutar da aka cimma a kasar albarkacin Eid al-Fitr.
Kasashen sun kuma yi kira ga duk wadanda abin ya shafa da su dora daga wannan mataki.
“Muna masu sha’awar ganin wadanda abin ya shafa sun dora kan wannan hobbasar cikin ‘yan kwanaki da makwannin da ke tafe, saboda ba tare da bata lokaci, a shiga tattaunawa sosai kan Afghanistan da zimmar cimma zaman lafiya mai dorewa, wanda zai kawo karshen tashin hankalin da ake yi a Afghanistan,” a cewar takardar ta hadin gwiwar.
Kasashen da suka rubuta takardar sun hada da kasashen Qatar, Jamus, Indoneshia, Norway da kuma Uzbekisytan.
Wannan takardar ta biyo bayan wata sanarwa da reshen Afghanistan na kungiyar Taliban ya yi, cewa zai dakatar da kai hare-hare na tsawon kwanaki uku daga ranar Lahadi.
“Saboda ‘yan kasarmu su samu gudanar da shagulgulan Sallar Idi cikin sauki da kwanciyar hankali, Hukumar Masarautar Musulunci ta Afghanistan, ta yi kira ga dukkan mayaka da kada su kai hari kan abokan gaba a duk inda suke,” a cewar takardar ta Taliban.
Facebook Forum