Jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin da aka sassauta dokar hana zirga-zirga amma kuma an tsaurara matakan hana shiga ko fita jihar da kuma hana daukar fasinja fiye da biyu a motocin daidaita sahu wato Keke NAPEP.
A jawabin da gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yi wa al'ummar jihar ta kafofin yada labarai, ya bada umurnin a kwace duk wata mota da ta shigo da fasinja jihar, sannan su kuma wadanda ke cikin motar za a killace su tsawon makonni a bakin iyakokin shiga jihar.
DSP Sulaiman Yahaya Nguroje, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu sun kama motoci biyu da suka yi yinkurin shiga jihar.
Hadakar kungiyoyi masu sana'ar kabu-kabu da masu Keke NAPEP sun dauki matakan yi wa mambobinsu gargadi. Daya daga cikin shugabanin kungiyar ‘yan Keke NAPEP a jihar Adamawa, Kwamared Bashir Muhammed Jimeta, ya ce su da mambobinsu sun dauki matakan bada tazara da bin dukkan ka’idojin da gwamnati ta gindaya musu.
Ya zuwa yanzu dai ba a samu rahoton bullar cutar coronavirus a jihohin Adamawa da Taraba ba yayin da bincike ke nuna cewa duk da gargadin da ake yi akwai masu kunnen kashi da basa kulawa da bada tazara da rage zirga-zirga.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum