A karon farko a Najeriya an samu karin masu dauke da cutar coronavirus da yawansu ya kai 30 a rana guda. Matakin da masana kiwon lafiya ke alakantawa da fara yin gwaji gida-gida da gwamnatin Legas ta bullo da shi.
Rahoton da cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa wato NCDC ta fitar a baya-bayan nan ya nuna cewa masu dauke da cutar coronavirus sun kai mutum 373 a kasar, an kuma sallami wasu su 99 daga asibiti sai kuma wasu su 11 da suka rasu.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Legas ta ce ta gano mutane 119 dake nuna wasu alamu masu kama da cutar coronavirus, a sakamakon tsarin bi gida-gida da ta fara aiwatarwa wanda yanzu haka ya kai ta ga gidaje dubu 118 a birnin Legas.
Wannan na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da masana harkokin kiwon lafiya suka yi ga hukumar NCDC ta Najeriya akan ta fadada tsarinta na gano masu dauke da wannan cutar, wato ba sai mara lafiyar da ya kai kansa asibiti ba, zuwa ga yin gwaji ga kowa da kowa domin taka wa cutar birki. In ba haka ba, hatta zaman gidan da gwamnati ke umartar a yi ba zai magance cutar ba a cewarsu.
Masanan na fargabar akwai masu dauke da wannan cuta da dama a kasar, amma kuma rashin gudanar da gwaji yasa ba a gane su kuma suna ci gaba da yada cutar a tsakanin jama’a.
A jihar Neja, an tabbatar da samun mutum daya dake dauke da cutar a cewar Alhaji Ahmed Matine, sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana na rigakafin cutar coronavirus a jihar.
Har yanzu jihar Legas ce ta fi yawan masu dauke da wannan cuta inda take da mutane 214, sai Abuja mai 58, Kaduna da Bauchi 6, sai katsina 5, Kwara da kano 4.
Gwamnatin Najeriya ta karbi gudummowar kayan aikin lafiya daga Majalisar Dinkin Duniya da suka hada da naurorin shakar numfashi wato Ventilator guda 50, da kayan sakawa na kariya domin ma’aikatan lafiya.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum