Rahotanni da shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa rayuka fiye da 25 sun salwanta bayan haka wasu kuma sun jikkata sakamakon wani sabon rikici da ya auku a tsakanin al’ummar Shomo da Jole a karamar hukumar Lau dake arewacin jihar Taraba.
Rikicin ya barke ne sakamakon wata takaddama da ta tashi a tsakanin al’ummomin biyu akan wani wurin kamun kifi, dama al'ummomin sun sha samun rashin jituwa a tsakaninsu a baya. Yanzu haka dai an tura jami’an tsaro don maido da doka da oda a yankin.
Duk da halin da ake ciki na annobar cutar coronavirus ko kuma COVID-19, ana samun rikice-rikice a jihar Taraba, domin ko kafin wannan rikicin na baya-baya, sai da rayuka suka salwanta a makon da ya gabata biyo bayan rikicin da ya auku a kudancin jihar a tsakanin al’ummar Tibi da Jukun, lamarin da masu fashin baki da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama ke ganin abun dubawa ne.
Kwamared Gambo Daud na cibiyar “Centre for Human Rights Advocacy,” kuma dan rajin kare hakkin bil'adama a jihar ya danganta abinda ke faruwa a jihar da sakacin shugabanni.
Da yake maida martani a wata sanarwa game da abubuwan dake faruwa a Taraba, Shugaba Buhari a ta bakin hadiminsa a fannin yada labarai, Garba Shehu, ya bukaci al’ummar jihar su yi karatun ta natsu.
A sanarwar, Shugaba Buhari ya yi mamakin yadda a yanayin da ake ciki za a samu wasu da ba zasu so zaman lafiya ba, abinda ya ce gwamnatinsa ba zata lamunta ba.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum