Gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar daga yau Alhamis, goma sha shida ga watan Afrilu zuwa ranar Lahadi, goma sha tara ga watan Afrilun.
Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya ce gwamnati ta saukaka dokar ne don ba jama’a damar fita su siya abinci.
Ya ce “bayan kwana hudu kowa zai koma cikin gida, idan aka saba doka zamu dauki mataki.”
“Ba mu hana mutane zuwa masallaci ko coci ba, sai dai bamu so a wuce mutum 50 a wuri daya,” in ji gwamnan.
Ya kara da cewa daga ranar Litinin, dokar za ta ci gaba da aiki na mako guda.
Wasu al'ummar jihar Filato sun bayyana wa Muryar Amurka yadda wannan dokar ya ke sasu cikin wahala.
A cewar wani, “wasu azumi ma suke yi saboda babu abin da za a ci.”
A bangaren bai wa jama’a tallafi kuwa, shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman ya ce sun fara raba wa mutane tallafi domin taimaka musu.
Ya zuwa yanzu dai babu wanda aka samu da cutar a jihar.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum