Tashin hankalin da ya barke a wurin bukin ranar haifuwar, ya yi sanadiyar kona gidaje da mota biyo bayan fada ta kaure tsakanin matasan dake halartan bukin da wani matashi ya shiryawa kansa, lamarin da ‘yan sandan jihar ke ci gaba da bincike akai.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Bauchi, DSP Kamal Datti ya musunta cewa wannan rikici yana da alaka da fadar kabilanci ko ta addini kamar yanda mutane ke yayatawa. Ya kuma ki tabbatar da ko fada ce a kan ‘yan mata, lamarin da yace bincike ne kawai zai tabbatar da gaskiyar maganar.
A tattaunawarsa da wakilinmu na jihar Bauchi, DSP Kamal Datti ya shaida masa cewa an kama mutane 76 bisa tuhumar da ake musu da hannu a cikin hargitsin kuma ana ci gaba da neman sauran masu hannu a wannan rikicin domin a hukunta su.
A cewar rundunar ‘yan sandan tuni an samu kwanciyr hankali wurin, yayin da jami’ansu ke ci gaba da sa ido a kan zaman lafiyar yankin. Hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi ta lashi takobin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a wannan tashin hankali.
Ga rahoton da wakilinmu a jihar Bauchi Abdulwahab Mohammed ya aiko mana:
Facebook Forum