Dakunan bahaya suna ceton rayuka idan akayi la’akari cewa najasar da bil adama ke fitarwa na yada cututtuka masu kisa, sabili da haka ranar dakunan bahaya na nufin zaburar da al’umma don daukar matakan takalar matsalolin tsabtar muhalli a duniya.
Bayanai sun nuna cewar duniya ba ta kan turbar cimma burin maradun karni na shida wajen tabbatar da wadataccen dabarar tafiyar da tsabtar muhalli mai dorewa ga kowa da kowa, ya zuwa shekara 2030, inda ke nuni da cewar a yanzu a fadin duniya akwai kimanin mutane biliyan hudu da basu da lafiyayyen dakunan bahaya, a yayin da mutane miliyan 892 suna bahaya ne a fili wanda hakan babbar illace ga lafiyar al’umma da wuraren zama dana ayyuka da abinci dama tattalin arziki.
A rahoton da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya yi nuni da cewar a duniya kasar Najeriya ita ce kasa ta biyu a yawan mutanen da suke yin bahaya a fili a yayin da kasar Indiya ke zama ta daya.
Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.
Facebook Forum