Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Gudun Hijirar Kamaru Sun Kai Dubu 30 a Najeriya


'Yan Gudun Hijira
'Yan Gudun Hijira

Kamar yadda alkaluman hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ke nunawa kawo yanzu yan gudun hijiran kasar Kamaru da tashe-tashen hankula dake da nasaba da batun yan aware, ya tilastawa guduwa suna barin garuruwansu sun kai dubu talatin.

Yanzu haka akasarin yan gudun hijirar na zaman dirsham a jihohin Akwa Ibom da Cross Rivers da Benuwai da kuma Taraba, wadanda suka hada da maza da mata.

Halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki, ya tayar da hankalin hukumar UNHCR, da kuma kungiyoyi fafutuka irinsu Progressive Mind For Development Initiative (PMDI).

Kwamrad Abubakar Abdul Salam, dake zama shugaban PMDI a Najeriya, ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kai dauki.

Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz ya tambayi shugaban hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya ta NEMA, Imam Abani Garki, ko suna sane da halin da yan gudun hijirar ke ciki, sai ya amsa masa da cewa suna sane, amma suna jiran gwamnatin tarayya ne.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG