Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kokawa A Kan Fyade Da Ake Yiwa 'Yan Gudun Hijira A Njeriya


Wata Mai Juna Biyu
Wata Mai Juna Biyu

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Najeriya na ci gaba da nuna damuwarsu game da zargin da ake yi a kan lalata da 'yan matan da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu da yanzu ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira, ta hanyar yi musu fyade.

Wani rahoto da aka fitar a baya yace kungiyar Human Rights Watch ta nuna bacin ranta na rashin yin abin da ya dace wajen kare irin wadannan matan da tabbatar da 'yancinsu da kuma tabbatar da sun samun ababen more rayuwar.

Kungiyar ta tattara bayanan a kan lalata da kuma yiwa ‘yan mata 43 fyade, wadanda suke zaune a sansanonin gudun hijira guda bakwai dake Maiduguri a jihar Borno.

An samu irin wannan labari a wani sansanin ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa, inda aka yiwa wata ‘yar gudun hijira dake da tabun hankali fyade, wanda yanzu haka ta samu juna biyu, lamarin da yasa kungiyoyin fafutuka ke cewa dole a gudanar da bincike.

Kwamared Abubakar Abdul Salam dake zama shugaban kungiyar Progressive Mind For Development Initiative, PMDI, yace akwai bukatar a sa ido a kan abubuwan dake faruwa a sansanonin ‘yan gudun hijira a Najeriya.

Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz ya tattauna da Imam Abari Garki dake zama jami’in hukumar agajin gaggawa a Najeriya NEMA a cikin wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG