Wasu boma bomai sun tashi a babban masallacin cikin garin Kano, wannan abun ya faru ne a daidai lokacin da Liman ya tada kabbaran sallar Juma’a a harabar masallacin Juma’a na tsakiyar birnin Kano.
Liman dai bai tsayar da sallah ba, sai wani bom in kuma ya sake tashi a cikin masallaci.
Shedun gani da ido sun bayyana cewar akasarin mutane da zasu mutu a wannan tashin boma boman zasu kasance cikin masu gudun ceton rai ne, ba cikin wadanda hadarin bom in ya sama ba.
Kuma labarai sun nuna cewar bayan sallah tayi nisa sai mutane suka fara jin harbe harbe wanda yasa wasu da dama suka bar sallah don gudun ceton rai. Amma dai harwazuwa yanzu babu adadin mutun nawa ne suka rasa rayukansu a wannan harin. Jami’an tsaro sunyi kokarin kaiwa wajen masallacin amma mutane sun hanasu zuwa, suka fara jifansu, amma daga bisani sojoji sun iso kuma kura ta lafa don tantance faruwar abun. Kuma babu wani bayani a hukumance.