Bayan korafe korafe musamman ma daga bangaren ‘yan adawa, Gwamnatin janhuriyar Nijar a karkashin jagorancin Firayim Minista Birji Rafini ta tsallake rijiya da baya da tsakar daren jiya, bayan ‘yan majalisun dokokin kasar sunyi wani zama kan batun rusa ta.
Wakilin Muryar Amurka a Janhuriyar ta Nijar, Abdullahi Mamman Ahmadu, wanda ya aiko da rahoton ya ce wasu ‘yan adawar kasar ce suka shigar da bukatar tsige gwamnatin, bias zargin yin almundahana da dukiyar kasa, yawan taka kundin tsarin mulk da sauransu da suke zargin gwamnatin da yi.
To amma dai gwamnatin ta samu kuri'u masu rinjaye a majalisar, abinda zai baiwa gwamnatin wata damar ta ci gaba da aikinta a kasar.
‘Yan adawar dai sun fice daga zaman Majalisar jim kadan bayan jefa kuri'ar, ba tare da sun tsaya sauraren sakamako ba. Kuma daga baya sun yi zargin an tafka magudi. Su kuma bangaren da ke goyon bayan gwamnati sun zargi ‘yan adawar da jefa Janhuriyar Nijar cikin rudun yinkurin rusa gwamnati, wanda su k ace ya haddasa asara ga kasar.