Bayan faruwar wasu abubuwa cikin ‘yan kwanakin nan da Majalisun Dattawa na Wakilai su ka bayyana da cewa karan tsaye ne ga tsarin dimokaradiyya daga bangaren Shugaban kasa da kuma bangaren tsaron kasar, Majalisar Dattawa ta ce ta bi sahun ‘yar’uwarta Majalisar wakilai wajen fara tsara kudurin tsige Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, a bisa wadannan laifukan da suka ce ya yi wa kundin tsarin mulkin Kasa.
Sanata Alkali Abdulkadir Jajere, ya tabbatar da yunkurin a wata hira ta musamman da yayi da Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda a Abuja.
Madina ta ce a makon da ya gabata Majalisar Wakilai ta ce ta fara tara sunaye domin yunkurin tsige Shugaba Goodluck Jonathan. Senata Jajere ya yi ikirarin cewa har da wasu ‘yan PDP da ke goyon bayan tsige Shugaban Nijeriya din saboda rashin iya Shugabancinsa musamman ta wajen yin barazana ga dorewar dimokaradiyya.
Ya ce kundin tsarin mulkin kasa na da muhimmanci ga ‘yan kasa da kuma dorewar dimokaradiyya. Don haka, y ace ya wajaba, ‘yan kasa su kare tare da mutunta kundin tsarin mulkin kasa kamar yadda ya wajaba ga Musuimi ya yi aiki da Alkur’ani Mai Tsarki da kuma yadda ya wajaba ga Kirista ya yi aiki da Baibul mai Tsarki. Ya ce haka ne kadai zai tabbatar da dorewar dimoradiyya.