Hukumomin Amurka sun ce kama wadanda suka ketare iyakar daga Mexico ba bisa ka’ida ba ya ragu da kashi 7% a watan Satumba, zuwa mafi karancin mataki cikin fiye da shekaru hudu.
Hakan na faruwa ne yayin da aka tunkari zaben shugaban kasa, inda dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya mayar da batun shige da fice a matsayin babban batu.
Hukumar kula da iyakaokin Amurka ta kama kusan mutum 54,000 a watan Satumba.
Wannan shi ne adadi mafi karanci da aka gani tun watan Agustan 2020.
San Diego ta sake zama hanya da ake yawan ketare iyaka ba bisa ka’ida ba.
Tun daga watan Satumbar bara, Hukumar kula da iyakar ta kama mutum miliyan 1.53, adadin da ya ragu matuka da wanda aka gani a shekarun baya.
Dandalin Mu Tattauna