Mutane daga jihohin Amurka 50 ne zasu kada kuri’a a zaben shugaban kasa na bana. Sai dai kuma, sakamakon jihohi 7 da ake fi sani da Swing States, wato wadanda suke kasancewa manuniya ga wanda zai yi nasara a zaben suke tasiri ga dan takarar da zai yi nasara a zaben. Jihar Arizon dake kudu maso yammacin Amurka bisa al’ada ta fi raja’a ga zaben ‘yan takarar jam’iyyar Republican, sai dai kuma Joe Biden dan Democrats ne yayi nasara a zaben 2020, sannan haka lamarin zai kasance a zaben shugaban kasa na bana, kuri’un kwalejin zaben jihar zasu yi tasiri.
Jihar Arizona tana da yawan mutane miliyan 7, wanda bisa al’ada suka fi raja'a ga zaben ‘yan takarar jam'iyyar Republicans.
Cikin shekaru 76 da suka shige, ‘yan takarar Democrats 3 ne kawai suka taba samun nasara a jihar dake kudu maso yammacin Amurka. Joe Biden yayi nasara da dan rata a 2020, sannan a bana ma ana kan kan kan takarar zabe a jihar.
A cewar Thom Reilly, farfesa kuma kwarare akan al’amuran demokradiyya da al’amuran ‘yan kasa a jami’ar jihar Arizona. Ya ce masu rajin ‘yanci sunyi imani cewa ‘yanci shine abu mafi mahimmanci a siyasa, sannan ana iya samun ‘yanci ne ta hanyar rage karfin ikon gwanati.
Reilly ya ce fahimtar abinda wannan rukunin masu zabe zasu yi abu ne mai wuya. Ya ce “Akwai kalubale tattare da bada hasashen wanda zai yi nasara, kasancewar inda mutane suka karkata kuri’un su a wannan zabe baya nufin cewa a nan zasu sake karkata kuri’un su a zabe na gaba ba. Sabo da haka yanayin yadda suke zabe yana sauyawa.
Dandalin Mu Tattauna