Mahukuntan Birtaniya sun himmatu sosai wajen agazawa Najeriya domin ta kawo karshen kalubalen tsaro musamman a arewa maso gabashin kasar tare da murkushe kungiyar Boko Haram.
Yace Birtaniya zata yi aiki kafada da kafada da gwamnatin Najeriya domin murkushe mayakan Boko Haram da nufin wanzar da zaman lafiya.
Mayakan Boko Haram sun hallaka mutane da dama kuma sun lalata dukiya ta makudan kudade. Sun tagayyara rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya a yankin arewa maso gabashin kasar. Yace saboda haka zasu baiwa Najeriya hadin kai ta fuskar soji da sauran dabaru da fasahar aikin tsaro.
Ministan na harkokin raya kasashe na kasar Birtaniya yace gwamnatin kasarsa zata cigaba da ayyukan tallafi da hukumominta ke yi a Najeriya musamman a bangarorin ilimi da kiwon lafiya da kuma sha'anin kasuwanci.
Bayan ya ziyarci gwamnan Kano a gidan gwamnati ya wuce wurin mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi a fadarsa. Minista Nick ya kuma ziyarci majalisar dokokin jihar Kano inda ya nanata manufar gwamnatin Birtaniya wajen karfafa ayyukan majalisun dokoki ta fuskar bada horon sanin makamar aiki ga 'yan majalisa a matakin tarayya da jihohi..
Ga karin bayani.