Matsalar ta fi yin kamari ne a tsakanin al'ummar Fulani dake zaune a yankunan karkara.
Malam Muhammad Shehu daya daga cikin shugabannin Fulanin dake jihar Neja yace lamarin ya kai har ana yiwa mutanensu kisan gilla.Yace yanzu sai a kira Bafullatani ya kai kudi ko a zo a yi mashi kwace a gida. Yace lamarin ya addabi Fulani. Ko wannan satin akwai wadanda aka dorawa biyan miliyan uku ko fiye kuma sai sun kai kudin. Wasu kuma sai a dauki lambobin yawar hannunsu a ce su kawo kudi.
Satar mutanen ta hada da kashesu. Malam Shehu ya bada misalin wanda aka kashe a Mashegu da kuma wani da aka sace a Kutigi yau fiye da wata guda ke nan. Haka ma aka kashe wani da da dare a wata karamar hukuma.
Al'ummar Fulani tace tana nan tana shirye-shirye matakin da zata dauka kamar yadda hukuma ta yi
Rundunar 'yansandan jihar tace tana da masaniya akan matsalar kuma tana iya kokarinta wajen shawo kan lamarin kaamar yadda kakakin 'yansandan ASP Bala Elkana ya shaida..Yace wani salo ne kuma barayin suka fito dashi bayan an shawo kan satar shanu. Suna kokari domin har sun kwato mata biyu da aka sace.
Ga karin bayani.