Hankula sun fara karkata ga 'yan Boko Haram da suka mika kansu akan shirin sauya masu ra'ayi da zummar mayardasu cikin jama'a.
Shirin zai wankesu daga ayyukan ta'adanci da suka aikata can baya saboda ana ganin wasunsu sun shiga kungiyar ne alatilas.
Wannan shirin ya sa gwamnatin Najeriya tare da hadin gwuiwar Tarayyar Turai fitar da sabbin dabaru na sauyawa 'yan Boko Haram din tunane.
Tuni rundunar sojin Najeriya ta kafa wani sansani na sauyawa 'yan Boko Haram akida.
To saidai kamar yadda kila ake zato ra'ayoyin mutane sun banbanta akan shirin. Malam Usman Santuraki mai yin nazari akan alamura ya tofa albarkacin bakinsa. Yace shirin yana da kyau aboda akwai wadanda basu da akidar Boko Hram da aka tilasta masu shiga. Amma akwai wasu kuma su ne tushen gina kungiyar. Kamata ya yi gwamnati ta yi takatsantsan akan wadanda suka ce sun tuba a tabbatar lallai tuban na gaske ne kada al'umma ta cutu.
Akwai wasu kuma da suke nuna dari-darinsu da shirin. Wani yace lokacin da suke kashe mutane basu tuna zasu tuba ba. Tana yiwuwa cikin wadanda suka tuban sun yi haka ne domin sun ga zasu shiga hannun hukuma inda za'a yi masu hukumci.
Tsarin na zuwa ne a daidai lokacin da daruruwan 'yan Boko Haram ke zubar da makamansu suna mika wuya ga jami'an tsaro saboda nasarar da sojojin kasar ke samu.
Wani malami dake cikin shirin taimakawa 'yan Boko Haram din yace suna samun nasara akan 'yan kungiyar. Yace da yawa suna bayyana suna tuba suna kuma yin nadamar abubuwan da suka aikata. Yace suna karantar dasu suna kuka da hawaye. Suna tunanen can baya an cutar dasu ko kuma sun cutar da kansu saboda basu fahimci yadda alamura suke ba.
Hukumomin kasa da kasa na ganin akwai bukatar shirin a kasashen dake fama da rikici irin na Boko Haram. Shirin ka iya kawowa 'yan ta'ada da suka mika wuya sabuwar akida ta rayuwa.
Ga karin bayani.