Shugaba Trump ya bayyana cewa "Jared na babban aiki ga kasar," abin da ya gaya wa jaridar New York Times kenan da daren jiya Lahadi. "Na yadda da shi matuka. Kusan kowa na mutunta shi a yanzu haka ma yana kan aiki ne kan wani shirin da zai samar ma kasarmu biliyoyin daloli. Bugu da kari, watakila ma mafi muhimmanci, shi ne shi mutum ne na gari."
Kushner, dan shekaru 36 da haihuwa, wanda ya mallaki wani kamfanin harkokin gidaje da ke New York, kafin ya kasance daya daga cikin ma'aikatan Fadar White House, na auren Ivanka, diyar Trump, wadda ita ma mai bayar da shawara ce a Fadar ta White House.
Kushner, a cewar wasu kafafen yada labarai da dama, ya yi yinkurin samar da wata kafar sadarwa ta boye da Rasha, bayan da ya gana da Jakadan Rasha a Amurka Sergey Kyslyak, a farkon watan Disamba.
Wasu masu fashin baki kan harkokin waje sun ce wannan yinkurin da aka yi, yayin da saura makonni Shugaba Barack Obama ya bar gadon mulki, ya tayar masu da hankali saboda hakan na iya kawo cikas ga tsaron kasa, hasali ma wasu 'yan jam'iyyar Dimokarat sun ce kamata a janye shaidar tanancewa ta tsaro da aka bai wa Kushener.
Facebook Forum