Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da ranar 7 ga watan Maris na wannan shekara, a matsayin ranar da za ta gudanar da mukabalar.
Kwamishinan yada Labaran jihar Kano Muhammad Garba ne ya shaidawa Muryar Amurka a yau.
Ya ce, malaman jihar ke da alhakin shirya wannan mukalabar, inda gwamnatin jihar ta shigo ciki, shi ne wajen samar da hanyar tabbatar da yiwuwar hakan, ta hanyar samar da wuri da lokaci da dawainiyar malamai.
Garba, ya kara da cewa za’a gudanar da mukabalar ne a fadar mai Martaba Sarki Kano - malamai kuma a nasu bangaren tuni suka gama shirinsu, inda shi ma Shehin Malami Abduljabbar Nasiru Kabara, tuni aka mika mishi takardar sanar da shi taron kuma ake sa ran ya gama shiri.
Malaman dai sun zabi wadanda za su zauna da shi, inda yake cewa taron ba zai wuce na mutane 35-40 ba.
Haka zalika, gwamnati za ta tabbatar da an saka mukalabar a gidajen radiyo domin al’ummar gari su ji yadda mukalabar ke wakana.
Idan masu sauraron na biye da mu a ranar 7 ga Fabrairun wannan shekara ne gwamantin Kano, ta dakatar da malamin daga gudanar da karatu a makarantarsa saboda da zarginsa da yin batanci ga Annabin (S.A.W.,) zargin da ya musanta.