Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalaman Sheikh Kabara Su Ka Sa Mu Daukar Mataki - Ganduje


Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara
Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara

Gwamnan Kano ya ce hakkin gwamnati ne ta samar da zaman lafiya a cikin al'umma. Hakan yasa gwamnatin Kano ta dauki mataki biyo bayan wasu kalamai na Sheikh AbdulJabar Nasiru Kabara.

Dalilan da suka sa Gwamnatin jihar Kano daukar matakin rufe masallacin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke bada sallah da gabatar da karatu su ne, "Kalaman shi na nuna kaskanci ga Annabin Rahma, Annabi Muhammdu {SA}" a cewar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, cikin wata tattaunawa ta mussamman da Muryar Amurka.

Matakin ya biyo ne bayan wasu malamai na jihar ta Kano, da suka ja hankali akan cewar, hakan na iya haifar da hatsaniya, don haka gwamnati ta ga cewar akwai bukatar daukar matakin. Za a ga cewar kalaman ba wai kawai sun tsaya a cikin jihar ba ne, sun watsu a duniya.

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Idan kuma aka lura za a ga cewar Sheikh Abduljabar, ya yi umurni da cewar kada wani ya je gidansa, har yake kwatanta irin yankan da za a yi wa duk wanda ya je gidan nasa. To kaga gwamnati ba za ta bari irin wadannan abubuwan su cigaba ba.

Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara
Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara

Kalaman nasa suna iya harzuka mutane su dauki doka a hannunsu, wannan yasa muka gaggauta daukar matakin da muka dauka. Shehin Malamin, ya roki gwamnatin ta Kano da ta ba shi damar yin mukabala da malaman jihar ta Kano, don ya kare kansa da kuma ire-iren furcinsa, wanda yake ganin cewar akan dai-dai yake.

Gwamnati ta amince da bukatar tasa, wanda suma Malaman sun yi maraba da jin hakan, inda suke bayyana cewar ai sun dade suna neman wannan damar. Gwamnatin na shiri tare da taimakon Masarautar Kano, don ganin an gudanara da wannan Muhadarar.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Lokacin Da Yake Gaisawa Da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a Filin Idi
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Lokacin Da Yake Gaisawa Da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a Filin Idi

Yanzu haka dai ba a tsayar da ranar da za a yi wannan mukabalar ba, amma nan bada jimawa ba, za a kammala duk wasu shirye-shirye da suka kamata, za a kuma sanarwa jama'a ranar da za a yi taron, da kuma ganin an yada shirin ta kafafen talabijin da radiyo ga masu bukatar kallo da saurare.

A saurari tattaunawar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da Mahmud Ibrahim Kwari a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:02 0:00

Karin bayani akan: Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara, Ganduje, Nigeria, da Najeriya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG