Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Da Ake Ciki Game Da Zaben Shugaban Kasar Amurka


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.
Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Har yanzu gwamnatin Amurka ba ta fara batun mika mulki ga wanda aka yi hasashen zai lashe zaben shugaban kasar Amurka ba.

Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da yin watsi da cewa an ka da shi a zaben Shugaban kasa, tare kuma da ci gaba da zirgin cewa an tafka magudi a zaben, ga dukkan alamu har yanzu gwamnatinsa ba ta fara taimaka ma zababben shugaba Joe Biden ba, game da matakin farko na karbar ragamar mulki.

Aikin wata cibiyar gwamnati da ke Washington, mai suna GSA a takaice, shi ne ta amince da kasancewar Biden a matsayin sabon shugaban kasa, sannan ta kuma fara tsara yadda za a mika ragamar mulki, wanda a hukumance kan faru ranar 20 ga watan Janairu.

Aikin cibiyar ne ta samar da ofis, ma tawagar karbar ragamar mulki ta Biden a dukkan sassan gwamnati, ta kuma taimaka wajen wasu ayyukan.

Wani mai magana da yawun cibiyar ta GSA, ya ce cibiyar ba za ta fara aikin mika ragamar mulkin ba, har sai an tabbatar da sahihancin nasarar Biden, to amma babu haske kan ko yaushe hakan zai faru, ganin cewa har yanzu ana ci gaba da kidaya kuri’un wasu sassa na kasar.

A wasu jahohi kalilan ne kawai har yanzu ba a san wanda zai fi cin kuri’unsu ba, tsakanin Trump da Biden, kuma mayan kafafen labarai sun ayyana Biden a zaman mai cin zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG