Ministan yace halin kashe mu raba da jami'an kwastan din keyi shi ne musabbabin karancin kudin dake shigowa daga hukumar kwastan a wannan lokacin idan aka kwatantashi da shekarun baya.
Furucin ministan kudin ya harzuka kungiyar kwastan matuka, wadda ta kira taron gaggawa domin mayarda martani. Ministan yace rabin kudin haraji ne yake shiga baitulmalin gwamnatin sauran rabin kuma sai jami'an su raba.
Dama can babban daraktan ma'aikatar awon kaya Kanar Isaka Usman a karshen wani taro da suka gudanar a karshen watan jiya ya bayyana daukan matakan hana ketare iyakokin Nijar da wasu kaya da suka hada da man girki da tumatirin gwangwani da shinkafa da garin sukari.
Kanar Usman ya yi la'akari da yadda wasu suke yin anfani da hanyar wajen yin fasakwaurin wasu kayan na daban.
Saidai kuma kungiyar jami'an kwastan tace matakin ya gagara zartaswa ga hukumomin ta Nijar.
A washegarin kafa sabuwar gwamnatinsa shugaban Nijar Muhammadou Issoufou ya bullo da wani shirin da aka sa masa suna "yaki da bulala" domin farautar mahandama da masu cin hanci. To saidai jami'an kwastan din basu gamsu da yadda shirin ke tafiya ba saboda ana samun cinkoson motoci dauke da kaya a wurin awo.
Ga karin bayani.