Daga tsakiyar watan Mayu da ya gabata zuwa farkon watan nan jaridar lukure ta bankado sunayen matan manyan mutane da suka hada da matar shugaban kasa Malita Issoufou da babban hafsan hafsoshin kasar Janar Seni Garba da shugabar kotun tsarin mulkin kasa Madame Kadijatu Li a jerin sunayen wadanda ake harsashen sun yi cuwacuwa a jarabawar jami'an kiwon lafiya.
Tuni dai aka soke sakamakon jarabawar a watannin baya sakamakon alkallar da ta dabaibayeta.
Bayan alkalin ya sauraresu na tsawon 'yan awoyi ya yanke shawarar tasa keyar 'yan jaridar zuwa gidan yari har zuwa lokacin da aka waiwayesu. Saidai an sallami mawallafin wata jarida, wato Sumana Idrisa Maiga da sharadin za'a waiwayeshi nan gaba kadan.
Shugaban kawancen kungiyoyin 'yan jarida Baba Alfa ya nuna rashin jin dadinsu akan matakin da kotun ta dauka. Yace mulkin Muhammadou Issoufou ya taka doka saboda an kai 'yan jarida gidan kaso ba kan ka'ida ba. Yace laifin da ake tuhumarsu dashi bai tabata ba tukunna.
Baba Alfa yace a gaban alkali ne mutanen da aka zarga da yin cuwacuwa suka bayyana sunayen wadanda suka sasu aikata abun da suka yi kafin 'yan jaridan su wallafa abun da aka fada a kotu.
Ya zuwa yanzu gwamnati ta suke bakinta akan batun. Amma kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar Alhaji Asumana Muhammadou ya yaba da matakin da alkalin ya dauka soboda wai 'yan jaridan suna neman batawa manyan mutane suna ne.
Ga karin bayani.