Galibin wadanda karancin abinci ya shafa mazauna karkara ne da aka kiyasta dubu dari biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali yayinda wasu miliyan daya da dubu dari tara ke cikin wani hali mai dan sassauci.
Rahoton ya bayyana ne a daidai lokacin da manoma suka fara ayyukan damina, yayi gargadin cewa idan ba'a dauki matakai ba lamarin zai ta'ayara tsakanin watan Yuni da na Agusta mai zuwa.
Kungiyoyin fararen hula sun fara kiran gwamnati ta dauki matakan tallafawa talakawan da abun ya shafa.
Hamidu Sidi Fodi shugaban kungiyar kulawa da rayuwa yace sun san akawai canjin yanayi. Sun san lokaci ya sake. Yace irin noman da ake yi da idan aka ce shi ne za'a yi yanzu ba za'a samu abinci ba. Kamata yayi gwamnati ta shiga cikin karkara ta horas da talakawa ta bayar da kayan aiki da takin zamani akan lokaci domin kawo karshen batun yunwa a kasar.
Wani abun dake zama matsala ga talakawa shi ne yadda farashin buhun hatsi yayi tashin goran zabi a kasuwanni kasar sakamakon gardamar da daminar bara ta zo wa yankunan da tun fil azar a kansu aka dogara.
Alhaji Sani Shekarau shugaban 'yan kasuwa masu shigo da kaya daga ketare yace saidai a yi hakuri domin farashin hatsin bana ya tashi ainun. Daga Maradi suke samun hatsi amma bana babu sai kasar Zamfara ake samunshi kadan kadan dalilin da ya sa ya yi tsada ke nan.
Gwamnatin kasar da ta tabbatar da rahoton ta bayyana matakan samar da cimaka kyauta ko kuma akan farashi mai rahusa. Jami'in gwamnati Yabilla Mamman ya jaddada hakan. Yace abun dake faruwa ba bakon abu ba ne a kasar kuma idan an shiga irin wannan hali gwamnati na daukan matakan shafewa mutane hawaye ta hanyar basu taimakon abinci ko sayar masu da cimaka akan farashi mai rahusa.
Tuni gwamnati ta saki tan tan na hatsi ga kasuwanni akan farashi mai rangwame.
Ga karin bayani.