Kasashen na Nijar da Chadi suna kokarin hada karfinsu ne domin toshe duk wata hanya da 'yan Boko Haram ke bi suna kutsawa kasar musamman ta bangaren Najeriya.
Dangane da cewa 'yan Boko Haram sun kwace Bosso ministan tsaron Nijar yace abun da mutane ke cewa ba gaskiya ba ne domin sojojin kasar suna Bosso.Dangane da wai sojojin Chadi sun isa Bosso ministan yace wannan ma ba gaskiya ba ne domin har yanzu basu isa kasar ba.
Yace aniyarsu da Chadi ita ce su yi tafiya tare su yaki kungiyar Boko Haram, su bisu har cikin Najeriya su fatattakesu domin kada su sake shiga Nijar ko Chadi. Ministan ya amince da kasancewar sojojin Najeriya a cikin Nijar a garin Bosso dake yankin Diffa.
Bayan ya dawo daga taron kungiyar kasashen yammacin Afirka renen Faransa da suka yi a Dakar babban birnin Senegal, Shugaban Nijar Muhammad Issoufou ya wuce zuwa kasar Chadi.
A Chadi ya gayawa takwaransa Idris Deby cewa a shirye yake su dauki duk matakan da zasu bada damar murkushe kungiyar kashe kashen bayin Allah. Yace zasu dage domin tabbatar da tsaron al'ummominisu na Chadi da na Nijar. Yace zasu hada karfi da karfe ta fuskar kayan yaki da musanyar bayanai don fatattakar haramtacciyar kungiya. Yace zasu yi duk abun da zasu iya yi su kawar da kungiyar Boko Haram daga doron kasa.
Shi kuwa shugaban kasar Chadi cewa yayi abun da ya faru a Bosso alama ce da ta nuna karara rashin hobasa daga kasashen dake cikin kungiyar yaki da Boko Haram. Yace an yi taron shugabanni har ba iyaka tare da kafa rundunar hadin gwuiwa wadda bata fara aiki ba. Saboda haka harin da kungiyar Boko Haram ta kai Bosso ba abun mamaki ba ne idan aka yi la'akari da wannan hali na gazawa a bangarensu shugabanni.
Shugaba Deby yace bai kamata su tsaya wai har sai sun mallaki wasu manyan kayan aiki ba. Mafi dacewa shi ne kasashen su tafi filin daga don kada su ba kungiyar Boko Haram damar baje kolinta a kasashensu. Yace zasu yi tsayin daka don kare al'ummominsu da iyakokinsu.
A wani halin kuma ministan tsaron Nijar ya sanar cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a garin Kabalewa jiya inda suka kwashi ganimar abinci kana suka juya komawa inda suka fito ba tare da taba kowa ba.
Ga karin bayani.