Wata wasikar da ministan man fetur din kasar Nijar ya aikewa takwaran aikinsa na kasuwanci ce ta bayyana wannan mataki da ake shirin dauka.
Idan har hakan ta yiwu, hakan na nufin matatar man za ta iya sayar da kashi 50 na man da aka hako ga duk wanda ta so.
Tuni dai kungiyoyin da ke hankoron ganin ana cin gajiyar arzikin karkashin kasa da kasar ta Nijar ke da su suka yaba da wannan mataki.
Yayin da wasu ke yaba wannan mataki wasu ko gani su ke kamata ya yi ma a sayarwa da ‘yan kasuwa hannayen jari a harkar ta mai.
A Nijar an jima ana takaddama tsakanin kamfanin na Soraz da na Sonidep bisa adadin man da ake tonowa da sayarwa.
Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma kan wannan batu: