Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Muhawwarar Cikin Gida Tsakanin ‘Yan Jam’iyar APC


Wasu gwamnonin jam'iyyar APC (Facebook/APC)
Wasu gwamnonin jam'iyyar APC (Facebook/APC)

Rikicin cikin gida a Jam’iyar APC, na kara ta’azzara inda bincike ke bayyana akwai Jihohi sama da goma da rikicin ya shafa.

Rikicin jihohin ya hada har da zuwa kotu domin hana rantsar da su bayan da aka gabatar da shugabannin a matakin Jiha. To sai dai kuma a wani matakin lalubo bakin zaren warware rikicin, uwar Jam’iyar ta kafa kwamiti a karkashin tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Senata Abdullahi Adamu.

Daga cikin Jihohin dake fama da rikicin a Jama’iyar ta APC, sun hada da Kano, Bauchi, Ekiti, Osun, Gombe, Delta da jihar Imo. Jigo a Jama’iyar APC a Najeriya Yahaya Idris Sulaiman, Magayakin Ajiyan Bauchi yayi tsokaci kan dalilan da ya haddasa rikici a Jama’iyar tasu. Ya ce ya na ganin laifin shugaban kasa da ya amince da rushe shugabancin jam’iyar daga matakin kasa har zuwa gundumomi ba tare da wa’adinsu ya cika ba.

A jihar Bauchi kuwa Jigo na Jama’iyar APC Hassan Sheriff, sarkin Arewan Bauchi ya je kotu inda kotu ta bada umurnin da ka da wani ya ce zai rantsar da wani mutum a matsayin shugaba ko kuma mai rike da wani mukami.

A halin da ake ciki kuma tawagar kwamitin sasanta ‘ya’yan Jam’iyar ta APC ya ziyarci Jihar Gombe inda shugaban kwamitin Senata Abdullahi Adamu ya shaida wa manema labarai cewa a Jihar Gombe an karbi korafi guda daya daga abokin aikinsu na Majalisar Dattawa Senata Danjuma Goje, wanda bamu same shi ba doin karin bayani game da batun.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab:

Ana Ci Gaba Da Muhawwarar Cikin Gida Tsakanin ‘Yan Jam’iyar APC
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00


XS
SM
MD
LG