Ofishin kula da hakkokin bil adaman, ya ce ana samun munana hotunan bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta kan yadda ake cin zarafin bil adama.
“Wadannan matasan dake yekuwar yin fyade a Imbonekure a Lardunan Burundi, babban abin damuwa ne, domin kiraye-kirayen na su na kara tabbatar mana da irin labaran da wadanda suka tsere daga Burundin suke fada mana.” In ji Rupert Colville, wanda ya yi magana da yawun kwamishina Zeid Ra-ad Al Hussein.
A lokacin da hoton bidiyon ya fito baina jama’a a karon farko, jam’iyar CNDD-FDD mai mulki ta ce bidiyon na jabu ne kuma ba a cikin kasar ta Burundi aka dauka ba.
Amma bayan da ta amince cewa bidiyon na gaske ne, jam’iyar ta ce matasa sun rairai wata waka a wani gangamin jam’iyar wacce ba ta kunshe da irin manufofin jam'iyar.
Amma Colville ya ce, a mafi yawan lokuta akan samu shugabannin jam’iyar a irin wadannan taruka inda ake raira wannan waka, wanda hakan ke nuna goyon bayansu.
Facebook Forum