Masana shari'a da kuma sauran al'umar jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, mahaifar dan takarar jam'iyar PDP Atiku Abubakar na ci gaba da maida martani dangane da hukuncin da kotun kolin ta yanke.
Jam'iyyar adawa ta PDP da Atiku ya yi takara a karkashinta, ta ce jam'iyyar ta yi mamaki da hukuncin da alkalan suka yanke a dan kankanin lokaci kamar yadda sakataren jam'iyyar a jihar Adamawa, Hon. Abdullahi Adamu Prembe ya bayyana.
To sai dai kuma, ga 'yan jam'iyar adawa ta APC a nasu bangaren, suna ganin hukuncin ya yi daidai.
Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar, Ahmad Lawal, ya ce yanzu za su shiga zawarcin tsohon mataimakin shugaban kasan don ya komo tsohuwar jam'iyyarsa ta APC, tun da shari'a ta kare.
To ko ya masana shari'ar kuma ke kallon yadda aka yanke wannan hukuncin? Barr Sunday Joshua Wigra lauya mai zaman kansa, ya ce ko ba komai akwai darasin dauka a wannan hukunci.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola: