Sarauniya Sally Kanu, mahaifiyar Nnamdi Kanu ta rasu a kasar Jamus a ranar 30 ga watan Agusta. Sakamakon haka, wadansu sarakunan gargajiya na kabilar Igbo a jihar Imo suke rokon gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi mashi afuwa, ta ba madugun kungiyar IPOB mai gwagwarmayar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu izinin dawowa gida, don yin jana'izar mahaifiyarsa.
Barista Uche Achi Okpaga kakakin kungiyar Ohanaeze Ndigbo, yace an taba yin haka lokacin da mahaifiyar Ralph Uwazuruike, madugun kungiyar MASSOB ta rasu yana tsare a gidan yari. Kuma aka roki gwamnatin tarayya da ta sake shi ya je ya yi jana'izarta, sai kuma gwamnatin tarayya ta amince ta bar shi.
Ya kara da cewa, Uwa tana da daraja sosai, saboda a mahaifarta take daukan danta tsawon wata 9, ta kuma kula dashi har ya girma, ya zama wani abu. Sai kuma ta mutu a ce ba a bada damar zuwa bata girmamawa ta karshe ba? Yace ai wannan zai sa mutum ya fidda rai, saboda haka, ya kamata gwamnatin tarayya ta dubi rokon da wadannan sarakan gargajiya suka yi, ta bar shi ya dawo ya yi jana'izar mahaifiyarsa.
Sai dai Mista Emeka Onah na ganin ya kamata a bar Nnamdi Kanu ya taka rawar kidar da ya fara. Yace bashi da ra'ayin cewa a bar shi ya dawo. Ya kamata ya fuskanci duk wani sakamakon da rikicin da ya janyo, ya haifar. Saboda haka, bai kamata a bar shi ba, ko kuma idan yana so a bar shi ya dawo, to fa dole ne sai ya nemi afuwa.
A cikin makon da ya gabata ne wadansu sarakunan kabilar Igbo, a karkashin jagorancin Eze Gideon Ejike suka bai wa Nnamdi Kanu sarautar Ihe Africa, wato Hasken Afirka, a yankin Orlu na jihar Imo.
Facebook Forum