Batun cin zarafin kananan yara ya ci gaba da bayyana a Najeriya inda a cikin makonni uku aka ceto kusan mutane dubu daya da suka hada da mata da kananan yara, wadanda ko dai aka sace, ko kuma aka gasawa akuba a wuraren da ya kamata a taimaka masu su iya zama 'yan kasa na kwarai.
Daga cikin wannan adadin akwai yara tara 'yan asalin jihar Kano da aka ceto a jihar Anambra inda wadansun su suka shafe kusan shekaru uku a wajen wadanda suke rike da su, wandanda suka sake masu sunaye da addininsu.
Ko a shekarun baya, an sami irin wannan rahoto inda wadansu daga kudu suka yi zargin an sace 'yarsu aka kaita arewacin Najeriya inda ita ma aka canza mata suna da addini, lamarin da ke daukar hankalin al'umma a ciki da wajen Najeriya.
Saurari cikakken shirin.
Facebook Forum