A yau Talata Sarkozy ya bayyana a gaban wata kotu, domin amsa tambayoyi kan zargin da ake mai na cewa ya hada kai da wani kamfani mai zaman kansa wajen boye yawan kudaden da ya kashe a lokacin yakin neman zabensa, wadanda aka ce sun wuce ka’ida.
Ana zargin tsohon shugaban kasar da kashe fiye da dala miliyan 25 da aka kayyadewa kowane dan takara a lokacin.
Sarkozy ya kasance shi ne shugaban jam’iyyar kwanzavativ wacce yanzu ake kiranta The Republicans, ya na kuma kokari ne ya daidaita kansa domin yin takara a zaben shekara mai zuwa.
Shi dai Sarkozy ya fadawa kotun cewa sam bashi da masaniyar badakalar boye yawan kudaden da ya kashe a kamfen dinsa.