Yau lahadi za’a fara zaben shugaban kasar Faransa zagaye na farko a kuri’ar da ake jin shugaba Nicolas Sarkozy zai sha kaye.
Sakamakon kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a da dama baya bayan nan sun nun shugaba Sarkozy yana baya ga babban abokin hamayyarsa mai ra’ayin ‘yan gurguzu Francos Hollande da maki mai dan yawa.
Haka kuma kuri’un sun nuna cewa Mr. Sarkozy zai sha kaye a zaben fidda gwani da za a gudanar ranar 6 ga watan gobe. Idan har hakan ya kasance Mr. Sarkozy zai kasance shugaban kasar Faransa na farko cikin shekaru 30 da zai sha kaye bayan kammala wa’adinsa na farko.
Mutane 10 da suke takarar shugaban kasa a Faransan, ‘yar takara Marine Le Pen tana sahun gaba na msu ra’ayin rikau, yayinda dan takara Luc Melenchon yake sahun gaba na masu ra’ayin gurguzu. Masu neman ra’ayin jama’a suka ce sai tayu wadan nan ‘yan takara biyu sune zasu sami lamba uku da kuma hudu. Ranar jumma’a duka ‘yan takaran suka kammala yakin neman zabe.
Ranar a jumma’a Mr. Sarkozy ya nemi gafara saboda irin matakai da ya dauka a farkon kama mulki. Yace kura kuran sun auku ne domin bai fahimci rawarda ofishin shugaban kasa ya kamata ya taka ba. Yayi alkawarin ba za’a sake fuskantar irinsu idan har ya sami nasara.