Hukumomin zabe sun ce jam’iyar ta National Front ta lashe tsakanin kashi 27 zuwa 30 cikin dari, baya ga jam’iyar tsohon shugaban kasar ta Nicolas Sarkozy mai matsakaicin ra’ayi, da ta zo na biyu kana sai jam’iyya mai mulki ta ‘yan gurguzu da ta zo ta uku.
An gudanar da wannan zabe ne a daidai da aka tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar, bayan harin da aka kai a watan jiya a birnin Paris da ya halaka mutane 130.
An dai yi hasashen cewa jam’iyar Marine Le Pen da ke kyamar baki za ta dara ta Socialist ko kuma masu ra’ayin gurguzu da ke mulki wajen karbuwa.
Rahotanni sun ce yanayin farin jinin shugaba Francois Hollande ya karu saboda irin tsauraran matakan da ya dauka tun bayan harin da aka kai a birnin Paris, sai dai farin jinin jam’iyyarsa ya ci gaba da raguwa.
Tun bayan da aka akai harin na birnin Paris ne farin jinin jam’iyar ta National Front ya karu, saboda shugabannin jam’iyar sukan alakanta matsalar ta’addancin da kasar ke fuskanta da kwararar baki cikin kasar.