Shugabar jam’iyyar, Marine Le Pen da wani da dan uwanta, Marion Marechal- Le Pen, sun sha kayi a kokarinsu na samun kuri’a u a wasu mahimman yankuna, yayin da jam’iyyar ta kuma sha kayi a wani yanki na uku a kasar ta Faransa.
A zaben zagayen farko da aka gudanar a makon da ya gabata, jam’iyyar ta National Front ta samu nasarar lashe zabuka a kanana hukumomi shidda cikin 13, amma a wannan zagaye na biyu, jam’iyyar tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da kawanyenta, sune suka lashe wannan zagaye na biyu.
Idan dai har aka tabbatar da wannan sakamakon zabe, hakan na nufin jami’yyar ta Le Pen ta sha mummunar kayi Kenan, wadda ke kokarin amfani da wannan zabe a matsayin ma’aunin da za ta yi takarar shugaban kasa a shekarar 2017, inda za ta kara da Sarkozy da kuma shugaba Francois Hollande.