Ofishin Hukumar ta lafiya da ke Guinea, ya kara da cewa, ana tsammanin mutane sama da 1,000 ne ake kallon suna dauke da cutar kuma ana saka musu ido.
Hukumar lafiya ta WHO, ta dauki wannan mataki ne na yin allurar rigakafin ga wanda ake tunanin ya yi mu’amulla da mai dauke da cutar, da sauran mutanen da shi kansa ya yi mu’amulla da su, bayan ta shi mu’amullar da mai dauke da cutar ta Ebola.
Jami’an kiwon lafiya na cikin gida a biranen Nzerekore da Macenta ne suka maido da wannan tsarin kawar da cutar, wanda aka yi amfani da shi a lokacin ana ganiyar barkewar cutar.
A farkon makonnan, hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cewa hadarin barkewar cutar ta Ebola a yammacin Afrika ya ragu, domin an rage barazanar yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya.