A ganin yan adawan gwamnatin shugaba Paul Biya bata da salon mulki mai kyau tare da nuna rashin adalci da nagarta a fadin kasar baki daya.
Shugaba Paul Biya ya kwashe shekaryu talatin da hudu yana gudanar da mulki ba tare da tabuka komi ba na abun a zo a gani. Yanzu kasar tana fama da rashin wadatacciyar wutar lantarki ba tare da gwamnatin ta yi wani abu ba. Haka kuma babu ruwan sha mai tsafta .Sha'anin tsaro kuma ya tabarbare. Harkokin ilimi da kiwon lafiya duk sun sukurkuce.
A cewar 'yan adawan gwamnatin kasar tana yiwa duk wadannan bangarorin rikon sakainar kashi tare da musgunawa 'yan adawa.
To saidai jami'an tsaro da magajin garin karamar hukumar Yaounde ta uku sun tarwatsa masu zanga-zangar yayinda suke ratsawa ta karamar hukumar.
Kakakin 'yan adawan ya nuna rashin jin dadinsa yayinda yake yiwa manema labarai jawabi. Yace shekaru uku ke nan da suka mika takardarsu amma gwamnatin kasar ta ki ta barsu fadin albarkacin bakinsu. Yace ba zasu yadda mulkin kama karya ya cigaba ba domin sun gaji. Sun kara da cewa ba zasu yadda da kiran da jam'iyyar dake mulki ta keyi na cewa shugaba Paul Biya ya zarce da mulki. Kakakin yace hararar banza ce su keyi. Cewa a yi zabe a wannan shekarar ba zata yiwu ba domin ba shekarar zabe ba ce.
A tsarin kundun mulkin kasar sai shekara ta 2018 ne zasu yi zabe. Masu mulkin kasar suna son su lalata dimokradiya a kasar aki daya tare da kira cewa a yi zabe wannan shekarar.
Falalu Mijinyawa na bangaren masu mulki kuma mataimakin shugaban karamar hukumar Yaounde ta biyu yace 'yan adawa sun yi maganar ruwa da wuta amma ba Kamaru kadai ba ce ke fama da wadannan matsalolin. Ana kokarin a gyara ruwa ba wai an bari ba ne kawai.
Ga karin bayani.