Mai yiwuwa ne a kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta bukata, a Sudan ta Kudu cikin makonni biyu masu zuwa, kamar yadda hukumar sa ido da tantancewa ta majalisar ta fada jiya Alhamis.
Festus G. Mogae, shugaban hukumar kuma tsohun shugaban kasar Botswana, ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, duk da saba ka’idojin tsagaita wutar da aka rika yi, an sami ci gaba matuka kwanan nan, da zai bada damar kafa gwamnatin rikon kwaryar.
Kimanin manyan jami’an kungiyar Sudan People’s Liberation Movement (SPLM) 230 daga bangaren hamayya ne suka koma Juba, babban birnin kasar tun ranar 24 ga watan Maris.
Yace kungiyar SPLM tace yanzu bata da wani sharadi na komawar shugabansu Reik Machar mukaminsa na mataimakin shugaban kasa a gwamnatin rikon kwaryar. Yace wannan yasa yake da karfin gwuiwa cewa za a iya kafa gwamnatin rikon kwaryar cikin tsakiyar watan Aprilu.