Shugaban Myanmar Win Myint, ya sanar yau Talata cewa ya yi afuwa ga fursunoni 8,500.
Wani mai magana da yawun gwamnatin kasar ya ce ahuwar da za a yi za ta shafi ‘yan kasashen ketare su 51 da kuma mutane 36 da wata kungiyar sa ido wadda mazauninta ke Thailand ta ce fursunonin siyasa ne.
Wannan umurnin bai shafi wasu ‘yan jaridar Reuter’s su 2 dake fuskantar tuhuma akan mallakar wasu takardun bayanan sirri na kasar ba. ‘Yan jaridar na hada rahoto ne akan mummunan farmakin soja da aka kai jihar Rakhine, wanda ya sa daruruwan Musulmin Rohingya tsallakawa zuwa kasar Bangladesh tun daga watan Agustan shekarar da ta gabata.
Facebook Forum