Daukan matakin da majalisar dattawa tayi ya biyo bayan rikicewar da harkokin tsaro suka yi a jihohin Yobe, Borno da Adamawa. Jihohin dai sun kwashi sama da shekara daya suna cikin dokar ta baci.
To sai dai masu kula da alamuran yau da kullum suna ganin kaddamar da yaki akan jihohin yanzu ka iya zama kalubale ga zaben kasa mai zuwa cikin 'yan watanni biyar masu zuwa.
Sanata Abdul Ningi mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa wanda shi ma daga jihar Bauchi yake, daya daga cikin jihohin arewa maso gabas, yace idan har sun bar yakin da Boko Haram ke yi ya cigaba to sun yiwa dokar kasar kara tsaye.
Wakiliyar Muryar Amurka ta jawo hankalin Sanata Ningi akan sashen kundun tsarin mulki da yace duk lokacin da kasa ta shiga yaki to ba za'a yi zabe ba. Sabili da haka shawarsu tamkar amincewa ne da hakan.
Sanata Ningi yace zaman lafiya ne ya kawo maganar zabe. Amma a duba yanzu mutane ne ke mutuwa, ba daya ba ko goma. A'a daruruka ne suke mutuwa. Wani kuma na maganar yana son ya zama shugaban kasa ko gwamna ko shi sanata. Yace bai kamata a hada batun rai da zabe ba. Sai da ran da mutanen za'a iya yin zabe. Kowane yankin kasar ake yaki dole 'yan kasar su bar komi su bari a gama yakin.
Sanatocin da suka fito daga Borno sun tabbatarwa majalisar cewa akwai kananan hukumomi goma sha uku a jiharsu da basa hannun gwamnatin jihar. 'Yan Boko Haram sun ce suna cikin kasarsu. Sun daga tutarsu a wuraren, sun nada sarakuna. Yace masu maganar zabe sun nuna basu damu da arewa maso gabas ba. Sanata Ningi yace ya tabbata idan da wani sashen kasar ne da an sa kai, an dauki matakai kamar yadda aka dauka akan yaki da cutar ebola. Abun dake faruwa a arewa maso gabas yakamata a san shi ma yaki ne. A fuskanceshi a gama dashi.
A bangaren majalisar wakilai maganar karbar bashin dala biliyan daya da shugaban kasa ya nema ta dauke masu hankali. Bashir Adamu shugaban kwamitin dake kula da harkokin tsaro a majalisar yace batun bashin na cikin abubuwan da suke so su tattauna da shugaban kasa idan sun samu zarafin zama dashi. Su na son su tabbatar menene aka son a yi da kudin. Suna son su tabbatar da cancantar abun da ake son a yi da kudin domin kullum suna samun korafi cewa suna saka kudi a harkokin tsaro amma basa zuwa wurin. Babu cigaba akan harkokin tsaro. Sai sun sami bayani gamsasshe kana su zauna su yi magana.
Akan cewa hafsan hafsoshin dakarun Najeriya sun dinga ba majalisar rahotanni akan lamuran dake faruwa sai Bashir Adamu yace basu samu sun zauna dasu ba domin hafsan soji da na mayakan sam duk sun koma Maiduguri domin kula da abubuwan dake faruwa. Rashin zuwansu ba da gangan ba ne.
Ga rahoton Medina Dauda.