Kawo yanzu babu wanda zai ce ga yawan 'yan gudun hijirar da suka shiga cikin Maiduguri inda yanzu an samu cunkoson jama'a sakamakon hare-haren da suka gujewa.
'Yan kungiyar Boko Haram na yawan kaiwa kauyuka da garuruwa hari suna hallaka mutane da dukiyoyinsu. Dalili ke nan da jama'a da dama suka bar gidajensu suna fake a sansanin 'yan gudun hijira da gwamnatoci suka tanada masu. Wasu kuma sukan samu su shiga gidajen 'yanuwansu ko abokanai.
Wannan mugun yanayin ya sa yawancin mutanen jihohin Borno da Yobe da Adamawa cikin wani halin kakanikayi domin duk wayewar gari ana samun kwararowar jama'a zuwa manyan birane.
'Yan gudun hijiran da suka fito daga cikin karamar hukumar Marte manoma ne amma dole suka bar gonakinsu. Wadannan kauyukan inda babu noma bana sun kawo fargaban karancin abinci a jihar kuma watakila ma da kasar. Wani Alhaji Abba daga Marte yace sha'anin noma ya samu matsala domin sun riga sun yi shuka har sun sa iri da taki amma dalilin rashin tsaro yasa sun gudu zuwa Maiduguri.
Alhaji Ali Shettima Marte shi ne shugaban kwamitin tallafawa 'yan gudun hijira da gwamnatin Borno ta kafa. Gwamnan jihar ya bada kayan abinci na kudi nera miliyan goma. Akan zargin wai an ba kwamitin kudi ne Alhaji Marte yace ba kudi gwamna ya bayar ba. Ya bada kayan abinci ne.
Ga karin bayani.