Mutanen biyu da babban sufeton ‘yansandan garin Bernardino, Jarrod Burguan ya bayyana sun hada da Syed Farook, dan shekaru ashirin da takwas da haihuwa, wanda haifaffen Amurka ne da kuma wata mace mai suna Tashfeen Malik, 'yar shekaru 27 da haihuwa.
Sufeton ‘yansandan ya ce mai yiyuwa ne mutumin da matar, ko dai mata da miji ne ko kuma suna shirin suyi aure. Kafofin watsa labarai biyu da suka hada da kampanin dillacin labaran AP da jaridar Los Angeles Times duk sunce Syed da Tashfeen mata da miji ne, har ma sun taba haihuwa.
Mr. Burguan ya ce shi Farook ma’aikacin sashen kula da lafiya na karamar hukumar mulkin San Bernardino ne a da, a lokacin da abin ya faru ana cikin shiryawa cibiyar kula da nakasassun liyafar kirsimeti. An ce Farook ya bar wurin da ake wannan shirin ne a fusace, ya je ya dawo da ita Tashfeen, kowannesu dauke da tarin bindigogi da albarussai iri-iri.
Daga baya jami'an tsaro suka gano Farook da Malik a wani gida a garin Redlands kusa da inda aka kai farmaki. An yi musayar wuta tsakanin 'yansanda da maharan wadda ta yi sanadiyar kashe Farook da Malik yayinda 'yan sanda ke bin su a mota. Dan sanda daya ya sami rauni amma ba mai barazana ga rayuwa ba ne.