An yi wata girgizar kasa mai karfin gaske a Arewa maso Gabashin Afghanistan tare da jijjiga wasu sassa na Tsakiya da Kudancin Asia a jiya Lahadi. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, wani mutum yamutu daga girgizar kasar.
Wanda ya auku a lardin nan mai yawan tsaunuka da ake kira Gilgit-Baltistan. To amma har yanzu ba wani rahoton da ya nuna jikkata ko wata asara daga kasashen da suka ji rugugin wannan girgizar kasa ba. Bargaron masana kasa na Amurka sun auna nauyin girgizar kasar da cewa ta kai nauyin awo 6 da digo 6.
Abin ya taso daga lardin Hindu Kush ne, inda zurfin da ta kwakware ya kai zurfin kilomita 210 daga kasa. An kuma ji girgizar kasar a biranen Kabul, Islamabad da New Delhi.
Inda aka ga mazauna gidajen wuraren suna ta tserewa zuwa kan tituna a lokacin da gidaje da gine-gine ke ta layin faduwa. A shekarar 2015 ne dai aka yi girgizar kasa a Pakistan da Afghanistan mai nauyin awo 7 da digo 5 wadda ta hallaka mutane sama da 400.