Hakan ya nuna cewa an samu karin yawan fararen hula da ke mutuwa ko kuma jikkata da kashi hudu a rikicin kasar ta Afghanistan.
Ofisihin Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido akan rikicin kasar ya ce wannan shekarar ta 2015, ita ce wacce aka fi samun mutuwar fararen hula tun da ofishin ya fara bi-biyan adadin mutanen da ke jikkata a shekarar 2009.
Ofishin ya kara da cewa yakin da ake yi a wuraren da fararen hula ke zaune da kuma hare-haren kunar bakin wake a manyan birane, suna daga cikin manyan ababan da suka haddasa mutuwar fararen hular a shekarar ta 2015.
Sai dai rahoton ofishin ya nuna cewa an samu raguwar jikkatar fararen hula da kashi 10 daga hare-haren da kungiyar Taliban ke kaiwa.