Asusun tallafawa kananan yara-UNICEF ya bayyana cewa, har yanzu akwai kananan yara da dama da ba a yiwa allurar rigakafin shan inna ba a Najeriya, duk da yunkurin da ake yi na yiwa kowanne yaro kasa da shekara biyar rigakafi kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.
Duk da yake adadin yaran da ba a yiwa rigakafin ba ya ragu idan aka kwantanta da adadin a watan Disamba bara, bincike ya nuna Jihar Kano tafi yawan kananan yaran da ba a yiwa allurar rigakafi ba, biye da Kebbi da kuma Jigawa.
Asusun UNICEF ya bayyana cewa, rashin isa ga kananan yaran a lokacin rigakafin shine dalilin gaza yi masu rigakafi, abinda kuma ya sa adadin yaran da ba a yiwa rigakafi ba ya kai kashi 66%.
Bisa ga cewar darektan sadarwa a fannin cutar shan inna na cibiyar UNICEF a Najeriyam Tommi Laulajainen, ba a tarar da yaran ne a lokacin rigakafi, sau da dama ko dai suna wurin wasan kwallo, da yake nesa da gida, ko kuma suna wajen wani buki a kusa da gida.
Bisa ga cewarshi, dalilin koma bayan shirin a fadin kasa baki daya shine, rashin bada hadin kai da wandasu iyaye ke yi inda wadansu suke hana a yiwa ‘ya’yansu rigakafi. Bisa ga rahoton kimanin kashi 38% na iyaye suna hanawa a yiwa ‘ya’yansu rigakafi a jihar Yobe, kashi 24% a jihar Katsina, kashi 41 kuma a jihar Borno.