Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Bincike Kan Kashe Wani Ministan Somalia


Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed
Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed

Gwmantin Somalia ta ce ta kaddamar da bincike a kan mutuwar Ministan Ayyuka da gyare-gyare, bayan da dogarawan tsaron wani jami’in gwamnati suka bindige shi har lahira.

Ministan yada labarai Abdirahman Omar Osman ya shaidawa Muryar Amurka cewar harbin da aka yiwa Abbas Abdullahi Sheikh Siraji a kusa da fadar shugaban kasa ya yi masa lahani sosai.

Siraji mai shekaru 31 a duniya, shine minista mafi karanci shekaru a wannan gwamnati da Fara Minista Hassan Ali Khaire ya bada sanarwar nadashi a cikin watan Maris. Marigayin yana cikin rukunin yan gudun hijiran Somalia da suka dawo kasar a bara daga sansanin yan gudun hijira na Dadaab.


Wasu shedun gani da ido sun shida mana cewar Siraji ya mutu ne sakamakon harbi da jami’an tsaron Auditor General suka yi a lokacin da suka bude wuta.

Shiko Auditor General Nur Jimale Farah yace jami’an tsaron nashi bas u yarda da motar dake bayansu ba saboda sun zaci yan kunar bakin wake.


Shiko shugabaMohamed Abdullahi Farmajo da yake ziyara a Habasha ya dora a shafinsa na Twitter cewar zai takaita ziyararsa ya halarci jana’izar ban girma ga minister Abbas. Sai dai ya Umarci shugaban hukumomin tsaro da su gudanar da bincike a kan wannan harin kuskure.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG