Hukumomin jamhuriyar Nijar sun yi kira ga masu hannu da shuni dasu aikewa Nijar da agajin gaggawa domin tunkarar karancin abincin jama’a da ta dabobi daman a irin suka da ake fama da su a wannan kasa sakamakon bala’in fari da na ambaliyar da aka fuskanta a damanar da ta gabata da kuma wasu matsalolin na daban dake da nasaba da tabarbarewar sha’anin tsaro a kasashe makwafta.
Mawuyacin halin da aka shiga a yankunan karakara a sakamakon karancin abinci yasa hukumomin Nijar, kiran taron gaggawa wanda ya hada wakilan gwamnati da na kungiyoyi da jakadun kasashen waje domin fahimtar dasu halin da kasar take ciki da kuma bukatar da ke da akwai na neman taimako domin cike gibin da ake fama dashi a yanzu.
Ministan cikin gida Bazun Muhammad, yace abinci da za a rabawa jama’a ya kama ton dubu hamsin da biyu na hatsi wannan kasar ta mallaki su kuma za a fara rabawa, yace abinda ya shafi abincin dabbobi nan ne akwai karanci domin ana bukatar ton dubu tamanin da biyar a cikin yanzu haka gwamnati ta mallaki ton dubu shida da dari uku, ya kuma kara da cewa akwai karancin irin suka inda yace kasar na bukatar don dubu goma sha biyar amma tana da ton dubu uku.
Faduwar darajan Naira da kuma a daya bangaren illolin da rikicin Boko Haram ya haifar a fannin noma sun karu akan tarin wasu matsalolin da suka yi sanadiyar hadasa babbar gibi a game dai bukatun jama’a.
Wakilan kungiyoyi da jakadun kasashe a wannan taron na gaggawa sun bayana aniyar hanzarta bada dauki domin fitar da jama’ar yankunan da wannan matsala ta shafa daga kangi.
Facebook Forum